Ultimate magazine theme for WordPress.

Amnesty: Harin Rann shi ne mafi muni a baya-bayan nan

172

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta ce harin da kungiyar Boko Haram ta kai a garin Rann da ke jihar Borno shi ne mafi muni.

A sanarwar da ta aike wa manema labarai, kungiyar ta Amnesty ta ce mutum 60 ne ake da tabbacin sun mutu a harin na ranar Litinin 28 ga watan Janairu.

Amnesty ta ce “Mun tabbatar da mutuwar mutum 60 a harin wannan makon da Boko Haram ta kai wanda kuma shi ne mafi muni.”

Kungiyar ta kuma ce, “Mun kuma yi nazari kan hotunan garin na Rann da aka dauka ta hanyar tauraron da Adam, inda aka kona mafi yawan garin”.

Kawo yanzu ba a samu martanin gwamnatin Najeriya ba a kan wannan batu.

Ta kara da cewa gine-ginen da aka kona din an samar da su ne a shekarar 2017 wanda hakan ke nufin akwai yiwuwar cewa matsugunin ‘yan gudun hijira ne wadanda rikicin ya raba da muhallansu.

Har wa yau, Amnesty ta ce shaidun gani-da-ido sun shaida ma ta cewa sojojin Najeriya sun janye daga yankin kwana 1 kafin harin.

A wani harin na 14 ga watan Janairu kuma Boko Haram ta kona gine-gine sama da 100 a garin, kuma hara-haren biyu na kwanan nan sun lalata kusan gaba dayan garin, inji Amnesty International.

Garin na Rann ya sha fama da hara-hare. Ko a 2017 rundunar sojojin Najeriya cikin kuskure ta kai hari kan sansanin ‘yan gudun hijra a garin.

Source BBCHausa.com

Leave A Reply

Your email address will not be published.