Ultimate magazine theme for WordPress.

Ba don kudi nake goyon bayan Atiku ba – Sani Danja Mintuna 18 da suka wuce Aika wannan shafi Facebook Aika wannan shafi Messenger Aika wannan shafi Twitter Aika wannan shafi Email Aika

128

 Sani Musa Danja, ya ce ba don kudi yake goyon bayan dan takarar shugabancin Najeriya Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP.

Ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da BBC, inda ya ce duk abin da suke yi “ra’ayi ne ya sa muke yi.”

Atiku Abubakar zai fafata ne da Shugaba Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC, wanda yake neman wa’adi na biyu a zaben watan Fabrairun 2019.

Dan wasan ya ce kashi 85 cikin 100 na masu goyon Atiku suna yi ne don ra’ayin kansu, “ko kuma gajiya da wannan gwamnati ko kuma neman mafita ko kuma saboda rashin jin dadin abubuwan da suka faru shekara uku da suka wuce,” in ji shi.

A wani bangare kuma yayi karin haske a kan cece-kucen da ake yi game da mai-dakinsa, inda aka ce tana goyon bayan jam’iyya mai mulki APC, shi kuma yana PDP.

Ya ce matarsa “ba ta goyon bayan APC kuma ba ma ‘yar siyasa ba ce.”

Danja ya ce tana da wata gidauniya da ke tallafa wa jama’a ne wace ke aiki a wani lokaci tare da uwar-gidan gwamnan jihar Kebbi ta APC.

Ana dai ci gaba da samun rarabuwar kai musamman a bangaren ‘yan wasan Hausa na Kannywood, inda wasu suke goyon bayan dan takarar APC Muhammadu Buhari wasu kuma na bangaren PDP Atiku Abubakar.

Leave A Reply

Your email address will not be published.