Ultimate magazine theme for WordPress.

Ba za mu yadda da katsalandan ba-Buhari

116

Gwamnatin Najeriya ta ce ba za ta amince da abin da ta kira shishigin kasashen waje a cikin harkokin cikin gidanta ba.da ta kira shishigin kasashen waje a cikin harkokin cikin gidanta ba.

Wata sanarwa da mai taimakawa shugaban Najeriya kan watsa labarai Malam Garba Shehu ya fitar, ta ce “mun yi watsi da duk wani katsalandan ko kuma wani tunanin da ke son cusa tsoro ko rusa sahihanci da karbuwar tsarin zabenmu.”

Gwamnatin Najeriyar ta ce za ta yi maraba da duk wani mai sha’war ganin an gudanar da sahihin zabe cikin kwanciyar hankali a Najeriya.

Wannan na zuwa ne bayan da kungiyar Tarayyar Turai da Birtaniya da kuma Amurka suka nuna damuwa game da dakatar da Alkalin Alkalan kasar, makwanni uku kacal kafin zaben Shugaban Kasa.

Shugaba Muhammadu Buhari, wanda yake neman wani wa’adi, ya dakatar da Alkalin Alkalai Walter Onnoghen a ranar Juma’a game da zarge-zargen saba dokokin bayyana kadarori.

Babbar jam’iyya adawa ta Najeriya PDP ta bayyana matakin a matsayin wani kama-karya, sannan ta dakatar da yakin neman zabenta na wucin-gadi.

Dakatarwar ta janyo cece-kuce, saboda idan har aka kalubalanci sakamakon zaben shugaban Kasar, Alkalin Alkalan ne zai taka mahimmiyar rawa wajen yanke hukuncin wanda ya lashe zaben daga karshe.

Tarayyar Turai da Birtaniya da Amurka sun bayyana damuwa kan cire Alkalin Alkalan, suna masu cewa matakin zai iya zama matsala ga zaben kasar.

Tawagar masu sa ido ta tarayyar Turai a zaben Najeriya ta yi kira ga dukkanin bangarori na siyasa su bi tsarin doka da kundin tsarin mulki ya tanadar.

Amurka da Birtaniya sun nuna damuwa ne kan yadda aka dakatar da Alkalin alkalan ba tare da amincewar majalisa ba.

Birtaniya ta ce wannan zai iya cusa shakku a ciki da wajen kasar kan muradin gudanar da sahihin zabe a Najeriya.

Amurka ta ce yadda dakatar da Alkalin Alkalan ya janyo suka game da cewa ya saba wa kundin tsarin mulki da kuma ‘yancin bangaren shari’a, hakan na iya kawo cikas ga alkawalin da gwamnati da ‘yan takara da jam’iyyun siyasa suka yi na tabbatar da ganin an yi sahihi kuma karbabben zabe cikin kwanciyar hankali.

Amma a martanin da ta mayar, fadar shugaban Najeriya ta ce a shirye ta ke ta tabbatar an gudanar da sahihin zabe amma ba za ta amince da katsalandan daga waje ba kan harakokin da suka shafi cikin gidanta.

Leave A Reply

Your email address will not be published.