Ultimate magazine theme for WordPress.

Kungiyar dattawan Igbo ta bukaci a zabi Atiku #BBCNigeria2019

64

Atiku Abubakar

Kungiyar dattawan kabilar Igbo da ke kudu maso gabashin Najeriya, Ohaneze Ndigbo, ta yi kira ga dukkan ‘yan kasar su zabi dan takarar jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, a zaben 2019.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya zabi Peter Obi, dan kabilar Igbo kuma tsohon gwamnan jihar Anambra, a matsayin mataimakinsa.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar ranar Alhamis, ta ambato shugabanta, Mr John Nwodo, na cewa sun dauki matakin ne bayan majalisar kolin Ohaneze Ndigbo ta tattauna a Enugu kan dan takarar da ya kamata su mara wa baya a zaben watan Fabrairu.

“A kokarinta na ganin an gudanar da siyasa mai tsafta, majalisar koli ta Ime Obi Ohaneze Ndi Igbo ta gana ranar Alhamis 24 ga watan Janairun 2019 kan makomar kasarmu. Bayan ta yi azari sosai kan manufofin kowanne dan takara musamman kan batun sake tsarin kasar nan da kuma bai wa yankin kudu maso gabas muhimmanci, Ohaneze ta ji dadin yadda PDP ta zabi danta Peter Obi a matsayin mataimakin shugaban kasa.

“Don haka take ganin dan takarar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ne ya dace ta mara wa baya saboda alwashin da ya sha na sake fasalin kasar nan, kuma ya jaddada hakan lokacin ziyarar da ya kai Amurka kwanan baya.”

Ba wannan ne karon farko da kungiyoyin addini da na kabilu ke mara wa wani dan takara baya ba.

Ko da a farkon watan nan, kungiyar Izala ta sanar da aniyarta na mara wa shugaba Muhammadu Buhari baya a zaben shugaban kasa da za a yi watan Fabrairu.

Sai dai wannan mataki ya raba kan shugabanni da ‘ya’yan kungiyar inda wasu shugabanninta suka bukaci mabiyanta su zabi Atiku Abubakar saboda, a cewarsu, shi ne dan takarar da ya fi tallafa wa musulunci.

Leave A Reply

Your email address will not be published.