Ultimate magazine theme for WordPress.

Buhari Ya ce Obasanjo Na Bukatar Likita Ya Duba Lafiyarsa

50

Gwamnatin Shugaban Najeriya ta mayar da martani kan wasikar da tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo ya fitar wadda a ciki ya soki lamirin gwamnatin.

Mallam Garba Shehu, kakakin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke nan ke mayar da martani a kan wasikar da tsohon shugaban kasar Cif Olusegun Obasanjo ya fitar a kan mulkin gwamnati mai ci gabanin zaben shugaban kasa da ke tafe a watan gobe.

Kakakin ya bayyana wasikar da tsohon Shugaban Kasa Cif Olusegun Obasanjo ya fitar a jiya a matsayin wani yunkurin wasu ‘yan siyasa da ba za su iya ja da Shugaba Buhari ba a siyasance sai dai su rika cin dunduniyarsa.

Sanarwar ta ce da alama tsohon shugaban kasar na bukatar kwararren likita ya duba lafiyarsa, inda ta yi masa fatan samun waraka cikin sauri:

“Shawara a gare shi, shi ne ya nemi likita, ya nemi magani. Muna yi masa fatan Allah Ya ba shi lafiya”.

Sannan sanarwar ta kuma bayyana Obasanjo a matsayin mai hassada saboda ya san Shugaba Buhari ya fi shi martaba a idan duniya, kamar yadda sanarwar ta ce.

Ta kuma ce Cif Obasanjo na juya wa duk mutumin da ya ga ba zai kyale shi ya yi abin da ya so ba, kuma ya fitar da wasikarsa ta sa a yau ne domin ya rasa mafita domin ci gaba da tatsar haramtacciyar dukiyar da ya saba yi a shekarun baya.

Kakakin shugaban na Najeriya ya kuma ce zaben shugaban kasa da za a yi a watan gobe zai kasance sahihi kamar yadda Shugaba Buharin ya alkarwarta wa kasar da duniya baki daya.

Ga yadda ya bayyana abin da ya kira makomar tsohon shugaban kasa Obasanjo da abokan tafiyarsa bayan an bayyana sakamakon zaben shugaban kasa da ke tafe:

“Abin da muke so mu nuna masu a nan shi ne, kayin da suka sha a wancan karon somin tabi ne, kuma wanda za su gani a zabe mai zuwa sai ya rugurguza su a siyasance.”

Ya kara da cewa, “Daga wannan lokacin ba za a sake jin kansu ba, domin karshen siyasarsu ta zo. Jama’a za su kada kuri’a luma za su yi masu kayen da ba su taba tsammanin zai same su ba.”

Leave A Reply

Your email address will not be published.